Jami’an da ke aikin tsaron gabar ruwan kasar Italiya na gudanar da wani gagarumin aikin ceto rayukan ‘yan cirani da ke cikin wasu jiragen ruwa da aka gano na fuskantar barazanar nutsewa a cikin tekun Bahar Rum. Mutum akalla dubu daya da dari biyu aka kiyasta na cikin jiragen da suka taso daga arewacin Libiya a kan hanyar shiga Turai.
Wata kungiyar mai zaman kanta ta kasar Jamus mai suna Sea-Watch International, wacce ta gano jiragen da taimakon fasahar zamani ta ce, an tura wa jiragen man fetur da ruwa, amma mahukuntan kasar Malta na kawo musu cikas a kokarin ceto mutanen. Kafin aukuwar lamarin na wannan Litinin, rahotanni na cewa, ‘yan cirani kimanin dubu biyu aka ceto daga gabar ruwan Italiyan tun daga ranar Jumma’ar da ta gabata.