Juma’ar da ta gabata ne saurayin nan Yunusa dahiru, wanda ake zargi da dauko wata yarinya ‘yar asalin Jihar Bayelsa Ese Charles Oruru zuwa garin Kano domin su yi aure, ya samu kansa bayan da ya shafe watanni shida cur yana zaman jiran shari’a a gidan maza da ke jihar ta Bayelsa, sakamakon gaza ciki sharuddan belin da aka gindaya masa.
Yunusa, wanda aka fi sani da Yellow, an zarge shi ne da dauko Ese daga Bayelsa zuwa Kano ba tare da iznin Iyayenta ba, lamarin da ya faru tun a watan Agusta na shekarar da ta gabata.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke a Babban birnin Jihar Bayelsa mai arzikin man-fetur, wato Yenagua ta ba da belin Yunusa tun watanni shida da suka gabata, amma sakamakon gaza cika sharuddan da aka gindaya sai a ranar Juma’ar da ta gabata ne saurayin ya samu kansa.
An gurfanar da Yunusa a gaban kotun ne bisa laifuka guda biyar, ciki har da na garkuwa da yarinyar da kuma yin lalata da ita, wanda hakan ya haifar da samun da a tsakanin masoyan biyu. Manyan sharudda guda biyu da suka zame wa Yunusa matsala su ne samo mutane biyu ‘yan asalin jihar Bayelsa da za su tsaya masa, kuma dole daya daga cikinsu ya kasance mai sarautar gargajiya, dayan kuma ma’aikaci a gwamnatin jihar Bayelsa.
Da yake zantawa da Aminiya a Kano bayan da aka sako shi sakamakon cika sharuddan, Yunusa ya bayyana cewa wannan tirka-tirka ta koyar da shi darussa masu yawa a rayuwarsa, haka kuma lamarin ya dada kyautata rayuwarsa ta yau da kullum.
Dangane da zargin da aka yi cewa da farko an rika musguna masa a gidan yarin, sai ya ce duk da cewa ya fito ne daga bangaren arewacin kasar nan kuma an kai shi gidan kaso da ke a kudancin kasar nan, hakan ba ta sa an nuna masa bambanci ba a gidan yarin.“Ana kula da ni kamar yadda ake kulawa da sauran ‘yan zaman kaso wadanda galibinsu ‘yan yankin kudancin Najeriya ne. a duk lokacin cin abinci za a ba ni a abinci kamar kowane dan zaman kaso, haka ma idan na bukaci wani abin biyan bukata na yau da kullum a kan ba ni ba tare da nuna min bambanci ba,” inji Yellow.
Hakan kuma ya bayyana cewa dangantakarsa da sauran ‘yan zaman gidan yari kamar dangantakarsa da sauran mutane take, domin a cewarsa, babu wani mahaluki da yake tsangwamarsa wai domin ya fito daga arewacin Najeriya ko kuma saboda laifin da ake zargin ya aikata.
Yellow ya ce, yana kyautata zaton hakan na da na nasaba da jajircewar da kungiyar Lauyoyi Musulmi ta yi ne, domin a cewarsa, kungiyar ce ta yi tsayuwar daka domin kare mutuncinsa.
Ya kara da cewa, ‘’duk da cewa gidan yarin ba a arewacin kasar nan yake ba, hakan ba ta hana ‘yan uwana musulmi su taimake ni ba. Ya ce
“Mambobin wannan kungiya su suka yi fadi-tashi tsakanin Kano da Bayelsa har sai da suka samu nasarar karbo ni a matsayin beli. Kuma a yanzu haka sun lashi takobin ganin cewa lallai sai an yi mini adalci a wannan shari’a.”
Yunusa ya kara da cewa, a hakikanin gaskiya wannan lamari ya koya masa darussa da dama, ciki har da wayon zaman duniya da kuma yadda ya kamata ya rika mu’amilla da sauran al’umma da addininsu ko kabilarsu, domin a cewarsa, da a baya ya kiyaye haka to da bai samu kansa cikin halin da ya shiga a yanzu ba.
Saurayin ya bayyana cewa, sakamakon darussan ya koya a wannan tirka-tirka, lallai rayuwarsa za ta canza a nan gaba, domin kuwa zai yi taka-tsantsan gaya wajen mu’amilla da sauran mutane.
“Da zarar na koma gida ina da yakinin cewa mahaifina zai bijiro min da al’amarin aure, domin tun lokacin da na je kauyenmu da Ese ya fara nema mini wata yarinyar a nan kauyen namu, sai kuma wannan lamari ya afku, don haka dole aka dakatar da maganar auren nawa, amma yanzu na tabbata wannan magana za ta sake tasowa kuma lamarin ba zai dauki lokaci ba za a kammala komai.”
Ya ci gaba da cewa, ‘’hakika ba zan iya bayyana irin farin ciki na ba game da beli da na samu, ina mika godiyata ta musamman ga kungiyar Lauyoyi Musulmi wadda ta shige gaba wajen kare mutuncina da kuma kwato min hakkina. Haka kuma ina mika godiya ta ga duk mutanen da suka taimaka da kudi ko addu’a har aka kai ga cim ma wannan nasara. Hakika ba zan iya saka wa duk wadanda suka taimaka min a wannan lamari ba, sai dai kawai in roki Allah Madaukakin Sarki Ya saka musu da alherinsa kuma Ya kara musu karfin gwiwar ci gaba da taimaka wa masu karafin karfi irina a duk lokacin da suka samu kansu a cikin irin wannan hali,” inji Yellow.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban kungiyar Lauyoyi Musumi rashen jihar Kano, Sheikh Mujiburrahman, ya bayyana cewa kungiyarsa ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kare mutuncin Yunusa da kuma tabbatar da cewa an yi masa adalci a shari’ar da ake yi yanzu haka.
Ya ce a lokacin da babbar kotun ta gindiya tsauraran sharuddan beli, Lauyoyin kungiyar ne suka yi kokari har sai da kotun ta sassauta sharuddan, amma duk da haka kungiyar ba ta iya cika wadannan sharudda ba har sai da wadansu bayin Allah guda biyu suka kawo wa Yunusa dauki ta hanyar gabatar da kansu a gaban kotun da zummar tsaya masa a matsayin wakilai. “Wani abin ban sha’awa, su wadannan mutanen watau mai sarautar gargajiya da babban ma’aikacin gwamnatin Jihar Bayelsa mai mataki na 16, ba musulmi ba ne, amma duk da haka suka ga dacewar su ceci rayuwar Yunusa. Wannan lamari ya ba mu sha’awa matuka, domin hakan ya nuni da cewa har yanzu akwai mutanen da suke kallon Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya ,” inji Mujiburrahman.
Shugaban kungiyar ya tabbatar da cewa lauyoyin kungiyar za su ci gaba da bibiyar wannan shari’a har sai an yi wa kowa adalci, domin a cewarsa yin aldalci ga kowa shi ne babban burin kungiyar.
Ita ma da take zantawa da Wakilinmu, Lauya Huwaila Muhammad Ibrahim, wadda ta yi tsayuwar daka wajen taimaka wa Yello tun a farkon lamarin, ta bayyana cewa a rayuwarta ba ta taba tsammanin za ta kare wani da namiji ba a kotu, domin babban burinta shi ne kare hakkin mata, amma a lokacin da ta tattauna da Ese a Kano kafin a tafi da ita Abuja,sannan daga bisani Bayelsa, sai ta fahimci cewa Yunusa na bukatar taimakon lauyoyi don haka ta yi alkawarin sai inda karfin ya kare a wannan lamari.
Lauya Huwaila bayyan cewa, za ta ci gaba da taimaka wa Yunusa har sai gaskiya ta yi halinta, domin babban burinta shi ne a bai wa mai gaskiya gaskiyarsa, mai laifi kuma a hukunta shi gwargwadon laifin da ya aikata.
“Mun sha wahala matuka wajen dawainiyar zuwa Bayelsa a duk lokacin da shari’ar ta taso. Amma sakamon taimakon da wadansu bayin Allah suka rika bayarwa mun samu nasara, har gashi an karbo Yellow a matsayin beli. Hakika mutane da dama sun ba da gudunmawa ta kudi da shawarwari wanda hakan kuma ta kai mu ga samun nasara.”
Shi ma mahaifin Yunusa, Malam dahiru Bala, da yake zantawa da Wakilinmu ta waya, ya bayyana farin cikinsa na ganin dansa ya dawo gida cikin koshin lafiya. Ya ce wani bawan Allah dan Jarida ne ya kira ni daga Kano ya shaida mini cewa an sako dana kuma jimawa kadan sai gashi ya zo gida tare da wadansu lauyoyi wadanda ya shaida min cewa su ne suke ta fadi-tashin a ganin cewa ya samu kansa. “Hakika ina cike da farin ciki yadda nag a dana ya dawo gida bayan da ya shafe watanni shida a gidan kaso yana zaman jiran-tsammani. Ina godiya matuka ga duk mutanen da suka taimaka mana har Yunusa ya samu kansa, ba ni da abin da zan saka musu sai dai in yi musu addu’a Allah Ya biya su,” inji mahaifin Yunusa.
A yanzu haka dai babbar kotun ta dage shari’ar har sai ranar 13 ga watan Satumba domin ci gaba da shari’ar.