
Jami’an Real Madrid za su tafi Jamus a ƙarshen wannan mako a yunƙurinsu na shawo kan Borussia Dortmund da ɗan wasanta na tsakiya daga Ingila Jude Bellingham, ɗan shekara 19, don taho kulob ɗin na ƙasar Sifaniya a bazarar nan. (Marca)
Ɗan ƙwallon tsakiya na West Ham daga Ingila, Declan Rice mai shekara 24, shi ne kan gaba a jerin ‘yan wasan da Arsenal take nema a bazarar nan. (Telegraph)
Ɗan wasan tsakiya na Manchester United ɗan ƙasar Brazil Casemiro mai shekara 31, shi kocin Bayern Munich Thomas Tuchel yake hari a wannan bazara. (Kicker)
Kocin na Bayern Munich, Tuchel yana kuma alla-alla ya sake gamuwa da ɗan wasan tsakiyar Chelsea daga ƙasar Croatia Mateo Kovacic, mai shekara 28. (Sport1)
Sai dai Bayern, ba ta da niyyar sayar da ɗan ƙwallonta na tsakiya mai shekara 20, daga ƙasar Holland Ryan Gravenberch da bazarar nan, duk da yake, Liverpool da Manchester United da kuma Arsenal na nuna sha’awa. (CaughtOffside)
Tsohon kocin Bayern Munich, Julian Nagelsmann yana gaba-gaba a jerin mutum huɗu da za su iya zama manajan Tottenham Hotspur na gaba, sai dai Bajamushen kocin mai shekara 35, na iya fin ƙarfin ƙungiyar. (Telegraph)
Aston Villa na nazarin ɗauko ɗan ƙwallo mai kai hari na ƙungiyar Brentford daga Ingila Ivan Toney, da ke da shekara 27. (Football Insider)
Ɗan ƙwallon gaban Fotugal Joao Felix ba zai koma Atletico Madrid a bazarar nan, daidai lokacin da ɗan wasan mai shekara 23 ke shirin tsawaita zaman aro da yake yi a Chelsea. (Sun)
Brighton na ƙoƙarin kammala sayen ɗan ƙwallon Brazil mai shekara 21; gwanin kai hari Joao Pedro daga Watford. (Fabrizio Romano)
Napoli ba za ta fara bin zaɓin sayen ɗan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 26, Tanguy Ndombele a cinikin dindindin kan yuro miliyan 30 daga ƙungiyar Tottenham ba. (Nicolo Schira)
Manchester United na shirin miƙa tayin sayo ɗan wasan baya na gefen dama daga ƙasar Brazil Vanderson, mai shekara 21 da ke buga wa Monaco ƙwallo, sai dai tana fuskantar gasa daga sauran ƙungiyoyin Firimiya Lig da ke nuna sha’awa. (RMC Sport via Sun)
AC Milan na bibiyar halin da ɗan ƙwllon gefe na Arsenal daga Ingila mai shekara 23, Reiss Nelson yake ciki, har zuwa yanzu dai bai sanya hannu kan wani sabon kwanturagi da Gunners ba. (Calciomercato via Football Italia)
AC Milan ɗin kuma na nuna sha’awa a kan ɗan wasan tsakiyar Chelsea daga Ingila Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 27. (90min)
Brentford da Fulham da kuma Brighton dukkansu na zawarcin ɗan ƙwallon gaba na ƙasar Ghana, Joseph Paintsil mai shekara, 25, wanda ya ci wa kulob ɗinsa Genk, zakarun ƙasar Belgium ƙwallo 14 a kakar nan. (Telegraph)