Real Madrid ta lashe Fifa Club World CupReal Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta doke Al Hilal 5-3 ta lashe Fifa Club World ta dauki na biyar na takwas jimilla har da na sauya fasalin gasar.

Morocco ce ta karbi bakuncin gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi da aka kammala ranar Asabar.

Real Madrid ta ci kwallayen ta hannun Karim Benzema da Federico Valverde da ya ci biyu da Vinicius Junior da shima ya zura biyu a raga.

Al Hilal kuwa ta ci nata kwallayen ta hannun Moussa Marega da kuma Luciano Vietto da ya zura biyu a raga.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like