
Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta sake yunƙurowa domin cimma burin farauto Erling Haaland mai shekara 22 daga Manchester City a 2024, lokacin da akwai damar iya barin kungiyar akan yuro miliyan 240, kamar yada yake kunshe a kwantiraginsa.(AS – in Spanish)
Bayern Munich ta yanke hukuncin korar kociyanta, Julian Nagelsmann mai shekara 35, wanda ake tunanin dan garinsu Jamus kuma tsohon kocin Chelsea Thomas Tuchel ke iya maye gurbinsa. (Bild – in German)
Tottenham na iya dauko Nagelsmann domin maye gurbin dan kasar Italiya Antonio Conte, mai shekara 53. (Football.London)
Chelsea da Manchester City da Newcastle United na zawarcin dan wasan Juventus mai shekara 19 Samuel Iling. (90min)
Dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 25, zai jinkirta sa hannu kan sabon kwantiragi a Manchester United har sai an tabbatar da sabbin mutanen da za su saye kungiyar.(Sun)
Arsenal ta bi sahun Leeds da AC Milan da Sevilla a farautar dan wasan Barcelona Ilias Akhomach, mai shekara 18. (Sport – in Spanish)
Liverpool na fuskantar barazana daga Manchester United a rige-rigen saye kocin Monaco Paul Mitchell, mai shekara 41. (Mirror)
Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na aiki a kan yarjejeniyar saye dan wasan Hajduk Split Luka Vuskovic amma ta na fuskantar barazana daga Paris St-Germain. (Fabrizio Romano)
Everton ta bi sahun Newcastle a farautar dan wasan Brazil mai shekara 19 Giovani, wanda ke taka leda a Palmeiras. (ESPN Brazil – in Portuguese)
Everton za ta sa dan wasan Neal Maupay, mai shekara 26, a kasuwa. (Football Insider)
Yiwuwar dan wasan gaba na Argentina Lionel Messi, mai shekara 35, ya koma Barcelona daga Paris St-Germain na sake fitowa fili. (90min)
Ana iya haramta Barcelona daga wasanni a wata kakar sakamakon binciken da Uefa ta bude a kan su kan bada cin-hanci. (Sun)
Dan wasan Manchester United Victor Lindelof, mai shekara 28, zai yanke shawara kan makomarsa a karshen kaka. (Mirror)
Ana sake nuna damuwa kan wadanda za su mallaki Manchester United. (Guardian)