
Asalin hoton, OTHER
Real Madrid ta kulla yarjejeniya da kungiyar Palmeras ta Brazil don daukar matashin dan wasa Endrick.
Matashin mai shekaru 16 na daga cikin yan wasan da ake tunanin zasu zama shahararru nan gaba kadan.
Da dama na ganin Endrick zai bi sahun shaharrarrun yan wasan Brazil kamar Ronaldo da Ronaldinho da Kaka da Neymar da kuma watakila Pele.
Sai dai ba zai fara buga wa Madrid din wasa ba sai 2024.
Hakan kuma ya faru ne saboda dokar hukumar kwallon kafa ta duniya, da ta hana kulla yarjejeniya da yan wasa a irin wannan mataki har sai sun kai shekara 18.
To amma daga Palmeras har Real Madrid ba bu wanda ya bayyana kudin da aka biya a cinikin, duk da dan wasan zai ziyarci filin wasan Bernebeau a Sfaniya mako mai zuwa.
Endrick ne dan wasa mafi kankanta da ya taba ci wa Palmeras wasa a tarihi.
Yana kuma daga cikin matasan da ke buga wa Brazil wasa a matakin yan kasa da shekara 17.