Real ta rage tazarar maki tsakaninta da Barca ya koma biyar daga takwas



Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da Barcelona, bayan da ta ci Valencia 2-0 a gasar La Liga ranar Alhamis a Santiago Bernabeu.

Real ta fara cin na farko ta hannu Marco Asensia a minti na 52, bayan da ya buga kwallon da kafar hagu ta fada raga.

Dan wasan Brazil, Vinicius Junior ne ya ci na biyu, kuma na 200 kenan a kungiyar.

Sai dai Valencia ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10 daga minti na 72, bayan da aka bai wa Gabriel Paulista jan kati, sakamakon dukan Vinicius da ya yi.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like