
Asalin hoton, Real Madrid FC
Real Madrid za ta fuskanci Osasuna a karawar karshe a Copa del Rey ranar 6 ga watan Mayu.
Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama na neman Copa del Rey na 20 a karawar da za su yi a filin wasa La Cartuja, wato na Sevilla.
Ranar Laraba, Real Madrid ta kai wasan karshe bayan da ta doke Barcelona 4-0 a Nou Camp a wasa na biyu a daf karshe.
Karim Benzema ne ya ci uku rigis, sai Vinicius Junior, wanda shine ya fara zura kwallo a ragar Barcelona.
A wasan farko a zagayen daf da karshe, Barcelona ce ta yi nasara da cin 1-0 a Santiago Bernabeu cikin watan Maris.
Osasuna ta kai wannan matakin bayan da ta fitar da Athletic Bilbao, karon farko da za ta buga wasan karshe tun 2005.
A wasan karshe da Osasuna ta buga a Copa del Rey a kakar 2004/5, Real Betis ce ta lashe kofin da cin 2-1.
Real Betis ce mai rike da kofin bara, amma ba ta kai labari ba a kakar bana.
Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31, sai Athletic Bilbao mai 23 da kuma Real Madrid mai 19 – Osasuna ba ta daukar kofin ba.
Barcelona da Real Madrid sun buga El Clasico karo biyar a bana, inda kungiyar Nou Camp ta yi nasara a wasa uku ta Santiago Bernabeu ta ci biyu.
Wasa biyar tsakanin Barcelon da Real Madrid a bana:
Copa del Rel Laraba 5 ga watan Afirilun 2023
- Barcelona 0 – 4 Real Madrid
La Liga Lahadi 19 ga watan Maris 2023
- Barcelona 2 – 1 Real Madrid
Copa del Rey Alhamis 2 ga watan Maris 2023
- Real Madrid 0 – 1 Barcelona
Sifanish Super Cup Lahadi 15 ga watan Janairun 2023
- Real Madrid 1 – 3 Barcelona
La Liga Lahadi 16 ga watan Oktoban 2022
- Real Madrid 3 – 1 Barcelona
Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
Ranar Asabar 8 ga watan Afirilu, Real Madrid za ta karbi bakuncin Villareal a wasan La Liga, kwana hudu tsakani ta kece raini da Chelsea a quarter finals a Champions League a Sifaniya.
Ranar Litinin 10 ga watan Afirilu Barcelona za ta kece raini da Girona a La Liga a Nou Camp.