
Asalin hoton, Real Madrid FC
Real Madrid za ta fafata da Al Ahly a daf da karshe a Club World Cup ranar Laraba a filin wasa na Prince Moulay Abdellah a birnin Rabat, Morocco.
Cikin kofi shida da Real ke takara a bana, bayan da take fatan lashe na zakarun nahoyoyin duniya na takwas jimilla.
Real wadda ke takarar La Liga da Copa del Rey da Champions League, an dauki Sifanish Super Cup a kanta a Saudi Arabia, bayan da Barcelona ta yi nasara.
Kungiyar Santiago Bernabeu ta fara kakar bana da lashe Uefa Super Cup daga kofi shidan da ta yi harin dauka a 2022/23.
Real za ta fuskanci kungiyar Masar, wadda ta ci wasa biyu a Morooco, wadda ta fara doke Auckland City 3-0 a wasan farko da cin Seattle Sounders 1-0.
Ba kungiyar da ta dauki Club World Cup da yawa fiye da Real Madrid, wadda ke harin na takwas jimilla.
Ta fara daukar Intercontinental Cup a 1960 bayan cin Peñarol sai a 1998 bayan nasara a kan Vasco de Gama da kuma a 2002 bayan doke Olimpia de Asunción.
Bayan da aka sauya fasalin kofin, Real ta yi nasara a 2014 a Morocco, kuma karkashin Carlo Anceloti a wasan karshe da San Lorenzo de Almagro.
Daga nan kuma Real ta dauki uku a jere, ba wata kungiyar da ta yi wannan namijin kokarin a tarihin Club World Cup.
Ta lashe a 2016 a Japan a karawa da Kashima Antlers da kuma a 2017 a Hadaddiyar Daular Larabar a wasa da Gremio da kuma a 2018 a dai Hadaddiyar Daular Laraba a wasan karshe da Al Ain.
Ranar Talata za a fara wasan daf da karshe tsakanin Flamengo ta Brazil da Al Hilal ta Saudi Arabia.
Sannan a buga neman mataki na uku da wasan karshe ranar Asabar a Morocco.