Rigima Ta Ɓarke Tsakanin Iyalan Abiola Kan Dukiyarsa Bayan Shekaru 25 Da Mutuwar Sa


Rahotanni daga Legas sun nuna cewa sabon rikici na neman ɓarkewa tsakanin ‘ya’yan attajiri kuma dan siyasar nan, marigayi M.K.O Abiola a kan dimbin dukiyar da ya mutu ya bari, kasancewa har yanzu ba a raba gadonsa ba bayan shekaru 25 da mutuwarsa

Tun da farko dai, daya daga cikin ‘ya’yan marigayin, Abdulmumini Abiola ya zargi manyan ‘ya ‘yan mahaifinsu wadanda suka hada da Kola, Deji da kuma Agboola da yin katutu kan harkokin kasuwancin mahaifinsu. Marigayin dai, shi ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 1993 amma gwamnatin soja ta wancan lokacin ta ki mika masa ragamar mulki, a karshe ma, ta garkame shi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

You may also like