Rikici Tsakanin Fulani Da Tibi Ya Shafi Mazauna Kauyukan Iyakar Kamaru, NajeriyaYAOUNDÉ, CAMEROON – Ba wai batun rikicin ‘yan yankin Ingilishi da sojojin gwamnatin Kamaru ba ne, batun rikicin kabilanci ne da jihohin Benue da Taraba a Najeriya da ke makwabtaka da Kamaru inda suka kwashe shekaru suna fama da shi.

Wani mazaunin kan iyakar ya ce a makon da ya wuce, a wani kauye, kimanin mutane goma sha biyar dauke da makamai sun shiga wani shago, suka kwashe abinci da abubuwan sha. Washe gari kuma a kan hanya an sake samun labarin wasu gungun ‘yan bindiga daga Najeriya a cikin sa’o’i 24 kacal, suka yi awon gaba da mutane 22 da ke wucewa don garkuwa da su.

Magajin garin kan wannan iyaka ya ce ya sanar da shugabanninsa kuma ya ce sun bashi kwarin gwiwa kan mayar da martani mai inganci daga hukumomin Kamaru don “gyara lamarin”.

A yankin Kudu maso Yammacin Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya, hukumar gudanarwar gundumar Akwaya ta rubutawa hakimin Manyu a farkon watan Maris inda take gargadi kan irin wannan kutse-kutse a garin Messaga Ekol a cikin watan Fabrairu. Anan kuma an dorawa Fulani makiyaya daga Najeriya alhakin, bayan kazamin fada da ‘yan kabilar Tiv.

A cewar hukumomin yankin, an kashe mutanen kauyuka da dama a bangaren Kamaru. Karamar hukumar Akwaya ta ba da shawarar kulla huldar diflomasiyya da Najeriya tare da karfafa tsaron iyakokin kasar.

A ranar Juma’a 7 ga watan Afrilu, a bangaren Najeriya, a jihar Benue, hukumomin yankin sun yi gargadin barkewar sabon rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Saurari cikakken rahoton Mohamed Ladan:Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like