Rikici tsakanin kabilu ya barke a Darfur | Labarai | DWMasu aiko da rahotanni sun ce bayan dauki ba dadi tsakanin kabilun biyu kura ta lafa a birnin bayan isar jami’an tsaro da gwamnatin Sudan ta aike domin kwatar da tarzomar tare kuma da ayyana dokar ta baci a yankin. 

A alkaluman da rundunar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dindin Duniya dake a yankin ta fitar ta ce a yayin tashin hankalin an kone akalla gidaje 50 kurmus kana kuma lamarin ya raba iyalai dubu hudu da matsugunensu.

Da ma dai an cika samun rikicin kabilu a yankin Darfour da ke Gabashin Sudan, kuma idan za a iya tunawa a shekarar 2003 yakin basasa ya barke a yankin wanda ya yi ajalin mutane da yawansu ya kai dubu 300 tare kuma da raba wasu miliyan 2,5 da matsugunensu.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like