
Asalin hoton, AFP
Masu makoki sun bayyana fushinsu a wajen jana’izar Nizar Issaoui da aka yi ranar Juma’a
Ɗan wasan ƙwallon ƙafar Tunisia Nizar Issaoui ya mutu sakamakon ƙunar da ya samu a lokacin wata zanga-zangar adawa da rashin adalcin ƴan sanda, kamar yadda iyalinsa suka ce, lamarin da ya sa ya cinna wa kansa wuta.
An gan shi cikin wani bidiyo da aka wallafa a intanet inda a ciki yake ihu cewa ƴan sanda sun zarge shi da ta’addanci bayan wata rashin jituwa tsakaninsa da wani mai sayar da kayan marmari.
A wani saƙo na daban, ya ce ya yanke wa kansa hukuncin kisa ta hanyar wuta.
An kuma samu kaurewar arangama a wajen jana’izar matashin mai shekara 35 ranar Juma’a a ƙauyensa Haffouz, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka sanar.
Ƴan sanda sun zargi Issaoui da aikata ta’addanci bayan da ya yi ƙorafin cewa bai iya siyan ayaba kan ƙasa da dinar 10 ba kan kilo ɗaya, ninki biyu na farashin da gwamnati ta saka, a cewar rahotanni.
A wani saƙon Facebook, ɗan ƙwallon ya rubuta: “Saboda saɓani da wani mai sayar da ayaba kan dinar 10, ƴan sanda suka zarge ni da ta’addanci. Ta’addanci saboda yin korafi a kan ayaba… Ba ni da sauran kuzari. Ƴan sandan su san cewa a yau za a zartar da hukuncin.”
Daga nan ne kuma ɗan ƙwallon ya cinna wa kansa wuta a wani ɓangare na nuna adawa.
An samu tashin hankali a jana’izar ɗan wasan yayin da masu zanga-zanga suka riƙa jefa wa ƴan sanda duwatsu yayin da su kuma jami’an suke watsa musu hayaƙi mai sa hawaye.
Tsohon ɗan wasan ƙungiyar US Monastir ta ƙasar Tunisia ne, kuma mahaifi ga ƴaƴa huɗu.
Ɗan uwansa ya faɗa wa ƴan jarida cewa Issauoi ya ƙone sosai kuma likitoci ba su iya yin wani abu na ceto rayuwarsa ba.
Matakin da ya ɗauka ya yi daidai da wata zanga-zanga da aka yi a 2010 lokacin da wani mai siyar da kaya a bakin titi Mohamed Bouazizi ya cinna wa kansa wuta.
Lamarin ya janyo zanga-zanga da ta kai ga hamɓarar da Shugaba Zine al-Abidine Ben Ali.
Shugaba Kais Saied mai ci, ya janyo ce-ce-ku-ce a 2021 lokacin da ya kori firaminista tare da dakatar da majalisar dokokin ƙasar.
Tun daga lokacin ya yi amfani da sabon kundin tsarin mulki wanda ya tabbatar da ikonsa.
Gwamnatin Tunisia ba ta ce komai ba game da mutuwar Issaoui.