Rikici Ya Kaure Tsakanin Bangarorin Boko Haram Biyu


Boko

 

Rahotanni na nuna cewa barakar da ta samu a kungiyar Boko Haram ta kara ta’azzara a sakamakon rikici da aka samu bangarori biyu na kungiyar.

Matsalar ta fara ne makonni biyu da suka gabata, bayan da ‘yan bangaren Al-Barnawi suka kai hari a kan mabiya Abubakar Shekau.

Izuwa yanzu, ba’a iya gano iya tsananin rikicin ba, da kuma irirn abun da ya haifar ba sakamakon rashin kyawun hanyoyin sadarwa na zamani a yankin.

Rikicin ya samo asali tun bayan da uwar kungiyarta ta IS ta sanar da Abu Mus’ab Al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar, ta kuma kira ta reshenta na yammacin Afirka, al’amarin da ya baiwa tsohon shugabanta Shekau haushi har ya balle daga kungiyar da shi da mabiyansa.

Shekau dai na zargin bangaren Al-Barnawi da cin amanar kungiyar, inda shi kuma Al-Barnawi ke zargin mabiya Abubakar Shekau da tsananta hare hare a kan mutanen da ba su ji ba su gani ba.

 

Mutane da dama na marhaba da wannan al’amari inda suke ganinta a matsayin wani abu da zai sakwarkwatar da kungiyar ta yadda hukumomin tsaro  za su murkushe su cikin sauki.

You may also like