Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Benue SEMA tace tayi rijistar yan gudun hijira mutum 80,000 bayan rikicin da aka samu tsakanin fulani makiyaya da manoma.
Emmanuel Shior, shugaban hukumar shine ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba.
Ya ce mutanen da suka rabu da gidajensu na sansanoni guda huɗu dake ƙananan hukumomin Guma da Logo. Kananan hukumomin da ake zargin fulani makiyaya da kashe kusan mutane 50.
Yan Najeriya da dama sun yi allawadai da kisan ciki har da shugaban kasa Muhammad Buhari wanda ya umarci Babban Sifetan Yan’sandan Najeriya Ibrahim Idris da ya koma jihar ta Benue.
Shior yace yan gudun hijirar suna zaune a sansanonin da gwamnatin ta amince da su dake Daudu,Tse-Gindei, Gbajimba dukkaninsu dake kananan hukumomin Guma da kuma Ugba.
“A yanzu abinda muka yi shine ɗaukar bayanan mutanen ba tare da yin amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa ba kuma mun yi rijistar mutane 80,000 a sansanoni huɗu dake jihar,”ya ce.
“Akwai yiyuwar zamu sake buɗe ƙarin wasu sansanonin saboda mun fara karɓar wasu yan gudun hijirar daga jihar Nassarawa wadanda suma rikici makamancin haka ya raba da gidajensu,”
Shugaban hukumar yace tuni gwamna Samuel Ortom ya bada umarnin samar da kayayyakin da mutanen ke buƙata da suka haɗa da abinci dama waɗanda ba abinci kamar su katifu da sauransu.