Rikicin Benue:Fulani na kare kansu ne daga barayin shanu a cewar Gololo


Garus Gololo shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a jihar Benue ya ce harin da aka kai ranar sabuwar shekara harin ɗaukar fansa ne kan satar shanu da ake wa Fulani.

Maharan sun kai hari kan wasu al’ummomi dake ƙananan hukumomin  Guma da Logo dake jihar inda suka kashe mutane akalla 20.

Amma Gololo yace Fulanin suna kare kansu ne daga barayi.

Da yake magana da gidan rediyon BBC, Gololo ya ce sama da shanu 1000 aka sace a Nengere wani gari dake jihar, dai-dai lokacin da Fulanin suke fita daga jihar zuwa jihar Taraba.

Ya kara da cewa rikicin ya barke ne lokacin da Fulani makiyayan ke ƙoƙarin kare kansu da kuma dukiyarsu.

Amma kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta nesanta kanta daga kalaman na Gololo.

You may also like