Rikicin Fulani Da Mutanen Gari Ya Jawo Asarar Rayukan Mutane 5 A jihar Niger 


Mutane hudu Sun rasa rayukansu a wani yamutsi da ya barke tsakanin Fulani makiyaya da kuma mutanen garin Tugan Malam, karamar hukumar Paikoro dake jihar Neja.

Fadan na zuwa ne kwana guda bayan wani rikicin makamancin haka ya jawo asarar rayukan mutane 21, a karamar hukumar Mokwa.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa fadan ya samo asaline sakamakon sabani da aka samu tsakanin Fulani da kuma mutanen gari a kasuwar garin.

A cewar wata majiya wani matashin bafulatani ne ya cakawa wani dan garin wuka lokacin da suke tsaka da musu,yayin da suka ga dan uwansu kwance cikin jini sai mutanen garin suka mai da martani tare da kashe Fulani hudu kafin a shawo kan lamarin.

Wakilin jaridar ta Daily Trust ya gano cewa mutumin garin da aka sokawa wuka ya mutu jiya da safe a wani asibiti da aka garzaya dashi domin samun kulawar gaggawa.

Amma rundunar yan sandar jihar  tace sabanin da ya janyo asarar rayukan mutanen hudu yafaru ne a wata mashaya.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Bala Elkana ya tabbatar da mutuwar mutane hudu a yamutsin.

You may also like