Rikicin Fulani: Mutane 6 Sun Rasa Rayukansu A Jahar Taraba


 

 

 

Rahotanni daga jahar Taraba na nuna cewa akalla mutane 6 sun rasa rayukansu, yayinda da wasu dama suka bata, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kabilar Tibi da Fulani a kauyen Dan Anacha.

Rikicin ya fara ne tun a ranar asabar, bayan da aka gano wasu gawarwakin Fulani guda biyu da aka kashe sannan aka yar da su a jeji al’amarin da ya sanya fulani suka kai harin ramuwar gayya kan ‘yan kabilar Tibi da suke zargi.

Duk da cewa ba a samu cikakken rahoto akan adadin mutanen da suka rasu ba, akwai hasashen cewa akalla mutane shida ne suka rasu, inda wata kafar yada labarai ma ta rahoto cewa adadin ya kai 24.

A wani rahoto da kafar yada labarai ta BBC ta rahoto, rundunar ‘yan sandan jahar sun bayyana dalilai uku a matsayin abun da ke haddasa rikicin.

A fadar su, Fulanin sun ce ana kashe masu mutane da dabbobi, sannan gwamnati ta ki daukar mataki duk da kwamitocin da ake kafawa, da kuma wani nadin sarauta da aka yi wa ‘yan kabilar Tibin ba bisa ka’ida ba wanda kuma yake kawo rashin jituwa tsakaninsu da baki.

Ko a watan Fabrairun bana ma, irin wannan rikicin ya afku a jahar, al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama.

You may also like