Rikicin Fulani:Saraki ya jagoranci sanatoci zuwa fadar shugaban ƙasa


Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya jagoranci abokan aikinsa zuwa fadar shugaban kasa dake Abuja a daren ranar Talata.

Ƴan majalisar da suka gana da shugaban kasa Muhammad Buhari sun bayyana masa  matakin da suka cimma kan kashe-kashen mutane a jihar Benue dama sauran bangarorin ƙasarnan baki ɗaya.

Tun da fari dukkanin majalisun biyu sun yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta ɗauki kwararan matakai kan waɗanda ke da hannu a kisan.

Haka kuma majalisar dattawan ta bawa babban sifetan yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris wa’adin makonni biyu kan ya kama wadanda ke da hannu a harin na Benue da ya jawo mutuwar mutane 73.

“Ka wai dai tuni ne, kun san mun zo nan da kakakin majalisar wakilai kwanaki biyu da suka wuce. Yau muka yi zaman majalisa na farko a wannan shekara. munyi muhara kan abu mara dadin ji da yafaru a jihar Benue,” ya fadawa masu ɗauko rahoto daga fadar shugaban kasa.

“Mun zo ne domin mu sanar da shugaban kasa kan wasu matakai da muka yanke musamman kan abin da ya shafi harkar tsaro.”

You may also like