Rikicin Indiya da Pakistan a yankin Kashmir na kara munana


 

 

Bayan harin da ya kashe sojojin Indiya 18 a farkon watan nan a yankin Kashmir, a ranar Alhamis din nan kuma an samu musayar wuta tsakanin sojin Indiya da na Pakistan inda akakashe jami’an sojin Pakistan 2.

An fara kama wani sojan Indiya da ya je wucewa ta kusa da shingen binciken ababan hawa na Pakistan.

Bangarorin 2 sun yi arangama inda dukkansu suke cewa, suna kokarin samar da zaman lafiya ne a yankin.

Rikicin ya kuma shafi huldar diplomasiyya.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Pakistan ta gayyaci jakadan Indiya a kasarta.

Jami’an diplomasiyyar ındiya sun sanarwa da jakadan cewa, za su mayar da martani kan duk wani hari da sojin Pakistan za su sake kaiwa.

Amurka kuma ta yi kira da dakatar da rikicin da ake yi game da yankin na Kashmir.

Kakakin Fadar White House Josh Earnest ya sanar da cewa, mai bawa shugaba Obama shawara kan tsaron kasa Ssan Rice ta bayyana cewa, ta gana da ta takwaranta na Indiya.

An dauki kusan shekaru 60 ana fafata rikici tsakanin Pakistan da Indiya kan yankin kashmir wanda mafi yawan mazaunansa Musulmai ne.

Kowacce daga cikin kasashen na ikirarin mallakar yankin na Kashamir.

Kasashen duniya kuma na tsoro kan lamarin ganin cewa, kasashen na Pakista da Indiya sun mallaki makaman Nukiliya.

You may also like