Rikicin IPOB: Gwamnan Abiya Ya Tabbatar Da Cewa Nmamdi Kanu Yana Kasar Ingila 



A yayin da ake ci gaba da ce ce ku ce a kan inda Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu yake, Tsohon Gwamnan Abia, Uzor Kalu ya tabbatar da cewa tuni Shugaban IPOB din ya tsare daga Nijeriya zuwa Ingila.

Tsohon gwamnan ya ci gaba da cewa ba kai tsaye Nnamdi Kanu ya isa Ingila ba sai da ya rabe ta  kasar Malesiya. Wannan ikirarin tsohon Gwamnan ya tabbatar da munafuncin kasashen Turai kan yadda gwamnatin Birtaniya ta nemi sanin inda gwamnatin Nijeriya ta boye Nnamdi Kanu alhali kuma yana cikin kasarta.

You may also like