Ga dukkan alamu karshen rikicin da ya addabin jam’iyyar adawa ta PDP na tsahon watanni ya zo karshe bayan da bangarorinta biyu suka yarda su ci gaba da aiki tare da juna a jiya Talata.
Kwamitin riko na jam’iyyar a karkashin shugabancin Ahmad Makarfi tare da bangaren Ali Modu Sheriff sun gana a jiya a babban birnin tarayya Abuja inda suka yarda su sulhunta kansu.
A taron manema labarai da bangarorin biyu suka yi a tare, sun bayyana cewa sun yanke hukuncin su hada kansu su kuma mayar da hankali wajen kawo adawa ingantacciya domin kare mutuncin Demokradiyya a Nijeriya.
Haka kuma bangarorin sun yarda su yi majar kwamitocinsu wanda zai shiga aikin sasanta suk wani rikici dake tsakanin mambobin bangarorin a fadin kasar nan.
Karanta Wannan: Jam’iyyar PDP na Yunkurin Dauke Hankalin Buhari – Lai Muhammad
Mataimakin shugaban bangaren Ali Modu Sheriff, Cairo Ojuogboh wanda shine ya karanto takardar sasantawar ga manema labarai ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su guji yi ko fadar wani abu da ka iya haifar da banbanci ko rikici a cikin jam’iyyar.
Wannan dai shine karo na farko da ‘yan jam’iyyar suka hadu suka yi wani abu tare tun ballewarsu a watan mayun bana bayan gamgamin taronsu da aka yi a garin Fatakwal.