Rikicin Jihar Taraba: Osibanjo Ya Kafa Kwamitin Bincike


 

Mukaddashin shugaban kasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya kafa kwamitin bincike kan rikicin da ta cigaba da ci a jihar Taraba.

Hamisu Ibrahim, Babban Mataimakin Mukaddashin shugaban kasa ne ya bayyana bayan zaman da aka yi akan batun, ya ce Farfesa Osibanjo ya gana da shugabannin hukumomin tsaro tareda Gwamnan jihar Taraba Darius Isiyaku, don gano bakin zare.

Farfesa Osinbajo, ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda wannan rikici na yankin Mambilla ya shafa.

Wani Kabiru Danladi Lawunti, da yake bayyani kan tashe tashe hankulan da ke tada zaune tsaye a arewacin Nijeriya, ya labarta cewa, rashin hukunta masu tada wadannan fitintinu yasa ake cigaba da fuskantar irin wannan rikice rikice wanda irinsa ta faru a Kaduna, Nasarawa, Filato, Taraba, Benue da sauransu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like