Rikicin Kasar Sudan Ta Kudu Yana Ci Gaba Lashe Rayukan Fararen Hula


 

Mahukuntan Sudan ta Kudu sun sanar da gano gawawwakin fararen hula goma sha biyar a gundumar Mangalla da ke arewa maso gabashin birnin Juba fadar mulkin kasar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Sudan ta Kudu Daniel Justine Bolo a jiya Alhamis ya sanara da cewa: Jami’an tsaron kasar sun gano gawawwakin mutane goma sha biyar kuma biyu daga cikinsu mata ne a gundumar Mangalla da ke nisan kilomita 75 da birnin Juba fadar mulkin kasar.

Daniel Justine Bolo ya kara da cewa: Goma daga cikin gawawwakin na ‘yan kasuwa ne da suke fataucin gawayi, sannan hudu daga cikinsu makiyaye ne, sai kuma sojan gwamnatin kasar daya.

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayyana cewa: Tun daga farkon watan Satumban da ya gabata zuwa yanzu akalla fararen hula 95 ne suka rasa rayukansu sakamakon bullar sabon rikicin siyasa a kasar.

You may also like