- Muna Goyon Bayan Yunkurin Sojoji —Gwamnan Ribas
- Kowa Ya Kauce, Za Mu Fara Kai Munanan Hare-Hare —Tsagerun Neja Delta
- Ku Kauce Wa Tashin Hankali —Dattawan Yankin
Takun saka a yankin Neja-Delta mai albarkatun mai ya samo asali ne tun a shekarun 1990’s a bisa ga zullumi da fargaba a tsakanin kamfanonin mai na kasashen waje da wasu daga cikin kananan kabilun Neja-Delta, wadanda ke ganin an mayar da su tamkar gugar yasa, musamman al’ummar Ogoni da Ijaw.
Hayagagar ta kabilanci da siyasa ta ci gaba da aukuwa ne a 1990’s, duk da komawa da aka yi a turbar mulkin Dimokuradiyya, da kuma zaben Shugaba Olusegun Obasanjo a 1999.
A bayyane yake yadda gasar mallakar rijiyoyin mai ta taimaka wajen ruruta wutar rikici tsakanin kungiyoyin kabilu da dama, wanda hakan ya haifar da girke dubban sojoji da ‘yan sandan kwantar da tarzoma a yankin.
- Satar Mai A Tafkin Guinea (2006-2016)
Tun daga watan Oktobar 2012 al’ummar Nijeriya suka fuskanci sababbin sace-sacen danyen mai. Daga lokacin zuwa 2013, Nijeriya ta zama kasa ta biyu mafi fuskantar barayin man fetur a Afrika, baya ga kasar Somaliya. Ana kyautata tsammanin kungiyar MEND da ke kokarin tabbatar da ‘yancin Neja-Dalta ce kashin bayan aika-aikar.
Zuwa Oktobar 2012 MEND ta samu nasarar kwace jiragen ruwa 12 da garkuwa da mutane 33, tare da kashe ma’aikatan mai hudu. Tun lokacin faruwar wannan lamarin, kasar Amurka ta turo sojoji domin su bayar da horo ga sojojin Nijeriya kan yaki a cikin ruwa domin yaki da barayin man. Duk da cewar sojin ruwa sun lakanci dabarun farmaki a ruwa, amma har zuwa yau a na ci gaba da samun yawaitar satar danyen mai a kusan kowane lokaci.
- Garkuwa Da Fararen Fata
Kungiyoyin tsagerun Neja-Dalta a Nijeriya, musamman ta MEND sun bayar da kaimi wajen garkuwa da ma’aikatan mai ‘yan kasashen waje. Sama da mutane 200 ne ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su daga 2006 zuwa yau, sai dai mafi yawansu sun samu ’yanci ba tare da wata matsala ko illa ba.
- Farmakin Sojoji (2008–2009).
A watan Agustan 2008 gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da wani shiri na kakkabe ‘yan ta’addan, ta hanyar sintiri a tashoshin ruwa da binciken kwakwaf a dukkanin jiragen ruwa na farar hula a yunkurin gano makamai, tare da kai hari a maboyar ‘yan ta’adda da dama.
A ranar 15 ga watan Mayu, rundunar soji, a karkashin hadin gamin gambizar sojojin hadin gwiwa suka kaddamar da hari a Neja-Delta. Hakan ya biyo bayan garkuwa da ma’aikata da dama. A lokacin dubban ‘yan Nijeriya ne suka gudu daga gidajensu kamar yadda wasu daruruwa suka mutu kan aika-aikar.
- Afuwa Ga ‘Tsagerun Neja-Dalta a 2009-2016
A hobbasar magance ta’addanci a yankin Neja-Dalta da samar da zaman lafiya da fahimtar juna a daidai lokacin da fashe-fashen manyan bututun mai ya tsananta; Gwamnatin Umaru ‘Yar’adua ta kaddamar da shirin afuwa ga ‘yan Neja-Delta a ranar 26 ga Yuni 2009, a wani shirin na kwanaki 60, ba tare da wani sharadi ba. A shirin wanda ya fara daga ranar 6 ga Agusta 2009, ya kare a ranar 4 ga Oktoba 2009.
Dubban makamai, kama daga bindigogi, nakiyoyi da jiragen yaki na ruwa da milyoyin albarusai ne matasan suka hannanta wa gwamnati. Hasali ma matasa sama da dubu 30,000 ne suka sanya hannu a yarjejeniyar daga watan Oktoba 2009 zuwa watan Mayu 2011, tare da musayar alawus na wata-wata, a wani lokacin kuma har da kwangila mai tsoka ta tsaron bututun mai da gwamnati ke ba matasan.
Duk da cewa an kara wa’adin shirin afuwa ga matasan, a wannan shekarar na mulkin Muhammadu Buhari, sabuwar gwamnatin na ganin tamkar karfafa cin hanci da rashawa ne, wanda akan hakan ake ganin shirin ba zai ci gaba ba. Ofishin karbar afuwar dai na da alhakin canza halaye da dabi’ar matasan, tare da janyo su a cikin al’umma, ta hanyar koya masu sana’o’i da daukar nauyin karatunsu a ciki da wajen kasar nan.
- ‘Crocodile Smile’ Zai tabbatar da Tsaro A Yankin Neja-Delta -Buratai
Shugaban Rundunar Sojin kasar nan, Laftanar Janar Tukur Burutai ya bayyana cewar shirin ‘Operation Crocodile Smile’ zai samar da ingantaccen tsaro a yankin Neja-Dalta ta hanyar samar da zaman lafiya. Kuma wannan ya faru ne a daidai lokacin da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya jaddada goyon bayansa ga sabon shirin na kalubalantar sha’anin tsaro a yankin.
Janar Burutai ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana a ranar Litinin a yayin da ya jagoranci manyan jami’an soji zuwa kai gaisuwar ban girma ga Gwamna Wike a fadar gwamnatin Jihar a Fatakwal, inda ya bayyana cewa shirin nasu an bullo da shi ne domin horas da sojoji dabarun yaki a yankin Neja-Delta
Shugaban Sojin ya bayyana cewa shirin na da manufar horas da sojoji dabarun gudanar da aiki a matakin kwararru na gudanar da aiki ba tare da fita a hurumin da doka ta tanadar ba.
Ya ce, wani alfanu da ke ga shirin, shi ne sojoji za su rika shiga tsakani a wurare mafi hadari da fuskantar kalubale da al’ummar yankin ke fuskanta. Yana mai cewa a yanzu haka rundunar sojin ta himmatu wajen gudanar da shirin bayar da tallafi a fannin kiyon lafiya a garuruwan Bille a Ribas, da kuma Nembe a Bayelsa.
- Muna Goyon Bayan Yunkurin Sojoji —Gwamnan Ribas
Gwamna Wike ya bayyana goyon bayansa ga shirin ‘Crocodile Smile,’ ya kuma bayyana cewar zai yi dukkan kokarin da ya kamata domin ganin an samu tsaro a Neja-Delta. Gwamnan ya bayyana haka yayin da yake mayar da jawabi a ziyarar da Shugaban sojin rasa, Tukur Burutai kai masa a ranar Litinin a Fatakwal.
Gwamnan ya bayyana cewa, “gwamnatin jihar Ribas tana goyon bayan shirin. Kwamandan barikinmu ya yi mani cikakken bayani, don haka mun alakanta kanmu da wannan shirin a bisa ga manufarsa ta tsarkake yankin Neja-Delta.”
Ya ce, gwamnatin jihar Ribas ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen bayar da goyon baya ga Hukumomin tsaro domin samar da yanayi mai kyau ga mulkin Dimokuradiyya. Inda ya ce, gwamnatinsa ta sayo sababbin motoci shida ga jami’an ‘yan sanda, kuma a yanzu haka suna shirin samar da jiragen ruwa na yaki guda goma ga rundunar sojin ruwa.
- Gargadin Sojoji Ga Matasan Neja-Delta
Hedikwatar tsaro ta kasa ta yi kakkausan gargadi ga al’umma kan yawaitar kungiyoyin Neja-Delta da ke ikirarin alhakin kai farmakin fasa bututun mai, tare da labewa da samar da ‘yanci a yankinsu wajen aikata barna.
A kwanan nan ne dai kungiyar ‘Niger Delta Greenland Justice Mandate (NDGJM)’ ta fito fili ta dauki alhakin fashe bututun mai na kamfanin mai na kasa NNPC. Har wa yau kuma kungiyar ta sake fitowa tana kira ga mazauna kusa da bututun mai da na gas da su tashi daga inda suke zaune domin nisanta kansu daga hare-harensu da ke tafe.
Hedikwatar ta tsaron ta bayyana cewa babu wata kungiya ko wani mutum da ke da dama, ko ‘yancin yin barazana, ko tursasa wa mazauna kowane yanki a Nijeriya da cewa su tashi daga mazauninsu bisa ga wata manufar tasu ta daban.
Sojojin sun nuna takaicin yadda duk da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka domin inganta tsaro da samar da zaman lafiya a yankin Neja-Delta, amma wasu tsageru sun himmatu wajen haifar da matsala da kawo tashin-tashina a kokarin haifar da yaki, wanda akan hakan Hedikwatar tsaron ta ce ba za ta lamunci aikata kowane irin ta’addanci a yankin ba.
Su ma dattawan yankin sun yi kakkusan kira ga matasan Neja-Delta da cewa su guje wa tashin hankali . Suna masu ba su shawarar cewa ba mafita ba ce kokarin da suke yi na haifar da tarnaki ga zaman lafiyar kasar nan.
A yau dai kusan shekaru 26 ke nan da tsagerun yankin suke ci gaba da cin karensu babu babbaka a yunkurinsu na tabbatar da ‘yancin al’umarsu da ke ikirarin gwamnatin tarayya ta tauye.
A daya bangaren kuma, gwamnatin tarayya na da dana yanzu na iyaka kokarinsu domin taka wa ta’addancin matasan burki, amma hakan na faskara, ta yadda a wasu lokuta sai kura ta lafa, sai kuma kwatsam ta sake tashi daga baya, wanda akan hakan jama’a ke sanya idanun ganin ko wannan gwamnatin ta Muhammadu Buhari za ta iya shawo kan ayyukan ta’addanci a yankin mai albarkatun man fetur, tare da samar da zaman lafiya da doka da oda?