Rikicin PDP:Emmanuel ya gana da Wike







Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya gana da takwaransa na jihar Rivers Nyesom Wike a Fatakwal babban birnin jihar.

Emmanuel da Wike dukkaninsu sun tsaya takarar zaben fidda gwani a karkashin jam’iyar PDP wanda Atiku Abubakar ya lashe.

Yayin da Emmanuel ya kasance daya daga cikin jagororin yakin neman zaben Atiku shi kuwa Wike da sauran abokan tafiysara sun kauracewa yakin neman zaben Atiku.

Karkashin kungiyar G-5 Wike da kuma wasu gwamnonin da zaben bai yi musu dadi ba sun cigaba da sukar Atiku tare da neman a sauke Iyorchia Ayu shugaban jam’iyar PDP.

Amma a ranar Asabar Emmanuel ya ziyarci Wike inda suka shiga wata ganawar sirri.






Previous articleBBC Hausa: Lafiya Zinariya: Ka’idojin da ya kamata ki bi wajen shayar da jariri




Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like