Rikicin Sojoji Da Ƴan Sanda Yayi Sanadiyyar Rayukan Mutum 4 A YobeA jiya ne aka yi musayar harbe harbe a tsakanin sojoji da ‘yan sanda a garin Damaturu da ke jihar Yobe inda ‘yan sanda uku suka rasa rayukansu sai kuma soja guda da ya mutu a yayin arangamar.

Da yake tabbatar da rikicin, Kakakin rundunar soja na jihar, Kanal Ko O Ohunsanya ya ce ana ci gaba da bincike game da musabbabin arangamar. Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan da sojoji suka sace wani Kwamandan ‘yan sanda wanda masu tsaron lafiyarsa suka yi wa wani Babban soja duka bisa rashin sani.

You may also like