Rikicin Tigray: Jiragen sama sun koma aiki tsakanin Addis Ababa da Mekelle



Habasha

Asalin hoton, Getty Images

Iyalai na kuka tare da sumbatar hasumiyar filin jirgin sama da ke Tigray a Ethopia, yayin da suka yi cincirindo don saduwa da ‘yan uwansu da yaki ya raba su, bayan shafe wata 18.

Yanyin abin tausayin, ya biyo bayan dawo da zirga zirga r jirage a tsakanin babban Birnin ƙasar zuwa Mekelle.

Birnin wanda ke da yawan al’umma da ya kai 500, 000an yanke shi da sauran sassan duniya sakamakon mummunan yaƙin da ya bake tsawon shekara biyu, da ya janyo asarar rayukan masu yawa, da raba sama da mutum miliyan daya da ‘yan uwansu.

Gwamnati da mayaƙan Tigray Liberation Front, suka saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan da ya gabata, wanda hakan ya bayar da damar jirin daukar fasinjoji komawa harkokinsu a tsakanin jihohin biyu.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like