Mahrez ya bayyana wa Sashen wasanni na BBC muhimmancin kyautar a gareshi. Ga zancen nasa: “To a gaskiya tana da muhimmanci sosai, saboda ni dan Afirka ne, kuma ina ganin wannan wani abu ne mai daraja matuka ga duk wani dan Afirka. Saboda haka na yi murna sosai, kuma ina alfahari da karbar kyautar”.
Wannan kyauta ce ta karkare banjintar da dan wasan mai shekaru 25, wanda tuni ya lashe Gasar Premier, aka kuma zabe shi Fitaccen Dan Wasa na Kungiyar Kwararrun ‘Yan Kwallon Kafa ta Duniya, a bana.
Mahrez ya yi fice saboda yadda ya ke sarrafa kwallo; ya fito ne daga wani dan karamin gari mai suna El Khemis a Algeriya, ya ba da mamaki a gasar Primiya.
Shi ne kashin bayan nasarar ban mamaki da Leicester City ta yi ta lashe gasar, inda ya ci kwallo 17, kuma ya taimaka aka ci 11, lamarin da ya sa kungiyar tasa ta yi abin da ba a taba tsammani ba kafin fara kakar.
A watan Mayu, Mahrez ya zamo dan Afirka na farko da ya lashe kyautar dan wasan premier da ya fi fice a kakar wasannin bara, shekara biyu kacal bayan ya koma Leicester daga Le Havre, a kan kudi dala 400,000.
Kwallo hudun da ya ci a wasanninsa biyar na farko a gasar da babu kamarta a Turai ta tabbatar da cewa Mahrez zai kai bantensa a matakin koli.
Ya kuma yi fice a dfagen wasannin kasa-da-kasa. A wasanni biyar din da ya buga wa Algeria, ya ci kwallo biyu kuma ya taimaka an ci biyar, sannan ya taimaka wa tawagar Desert Foxes samun gurbi a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka da za a buga a watan gobe.
Bugu da kari, hukumar kwallon kafa ta FIFA ta yaba da muhimmiyar rawar da ya taka a wasannin kwallo, ta hanyar sa shi a cikin jerin ‘yan wasan da aka ware don zabar Gwarzon Kwallon Kafa na Duniya – shi kadai ne dan Afirka a cikin ‘yan wasa 23.
Yanzu dai Mahrez ya shiga sahun manya, ciki har da Abedi Pele, da Jay-Jay Okocha, da kuma Didier Drogba, wadanda suka lashe kyautar Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC.
Kasancewar har yanzu yana da sauran kuruciya, Mahrez na da isasshen lokaci a gaba da zai ci gaba da burge masoya kwallon kafa, wadanda suka nuna yadda suke matukar kaunarsa.