Kwararren dan wasan kwallon kafar kasar Brazil, Ronaldinho ya shirya tsaf domin aurar mata biyu a lokaci guda.
Ana zargin dan kwallon mai shekaru 38 da rayuwa tare da yan matansa biyu Priscilla Coelho and Beatriz Souza a katafaren gidansa dake birnin Rio de Janeiro.
A cewar kafafen yada labarai na kasar, Ronaldinho wanda cikkaken sunansa shine, Ronaldo de Assis Moreira, zai auri abokan zaman nasa biyu a wani biki da za a gudanar a gidan nasa.
Auran mata biyu a kasar ta Brazil ka iya sawa a daure mutum har na tsawon shekaru shida saboda haka ana ganin bikin da za ayi zai kasance ne kawai taron biki da mata biyu amma a hukumance ba zai kasane aure ba.
Ana zargin tsohon da wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona da fara soyayya da Beatriz a shekarar 2016, amma ya cigaba da soyayya da Priscilla, wacce suka shafe shekaru suna tare.
A cewar rahotanni dukkanin yan matan biyu suna karbar kudin alawus daga hannun dan kwallon da yawansu ya kai fam £1,500.