Ronaldo, Messi, Maradona, Zidane Da Sauran Manyan ‘Yan Kwallon Duniya Na Da Dana Yanzu Zasu Buga Wasan Kwallo a AbujaZakaran ‘yan kwallon duniya Cristiano Ronaldo wanda ke wasa a kungiyar Real Madrid da abokin hamayyarsa na kungiyar Barcelona, Lionel Messi da tsohon dan wasan kasar Faransa kuma mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane da tsohon zakaran kwallon Afrika, Abedi Ayew Pele na daga cikin ‘yan wasan da za su ziyarci babban birnin tarayya Abuja domin buga wasan kwallon kafa da aka shirya kan yaki da ta’addanci da kuma safara.

 

Za a buga wasan ne a filin wasa na Abuja a ranar 21 ga watan Maris, 2017, a karkashin jagorancin kungiyar Nest2None Support Initiative’.
A yayin da yake yi wa manema labarai karin haske, shugaban kungiyar, Barista Ndukwe Sam Obu ya bayyana cewa kungiyar ta kudiri aniyar yin amfani da wasan kwallon kafa ne wajen jawo hankalin jama’a kasancewar harkar kwallo wata hanya ce ta hada kan al’umma.
Barista Ndukwe ya kuma kara da cewa tsoffin fitattun ‘yan kwallon duniya irin su Diego Armendo Maradona na kasar Ajantina, Ruud Gulit, Thierry Henry, Geoge Opone Weah, Kanu Nwakwo da Jay Jay Okocha na daga cikin wadanda ake sa ran za su buga wasan.

You may also like