Ronaldo ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2016Dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya lashe kyautar dan kwallon kafa na duniya da ya fi yin fice a bana, wato kyautar Ballon d’Or.

Ronaldo mai shekara 31, ya taimakawa Real Madrid lashe kofin zakaraun Turai a bara, ya kuma ci kwallaye uku da suka bai wa Portugal damar cin kofin nahiyar Turai a 2016.

Dan wasan na Real Madrid ya ci kyautar Ballon d’Or karo na hudu kenan, bayan 2008 da 2013 da kuma 2014.

A tarihin lashe kyautar Lionel Messi ne ke kan gaba, wanda ya karbi guda biyar a shekarar 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da kuma 2015.

You may also like