An bayyana sunan Cristiano Ronaldo a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya, na Fifa na shekarar 2016.
Bikin Bada kyautar wanda aka bayar a jiya litinin a garin Zurich ya nuna cewa Gwarzon dan wasan kasar Portugal kuma mai bugawa Kungiyar Real Madrid Wasa Wato Cristiano Ronaldo ya Lashe gasar inda ya Buge abokan karawarsa Lionel Messi na Kasar Argentina mai Bugawa Kungiyar Barcelona wasa da kuma Antonio Griezman dan Kasar Faransa mai Bugawa Atlentico Madrid wasa.
A cewar Ronaldo, shekarar 2016 ta kasance kamar mafarki a wajensa inda ya jagoranci kasarsa ta Portugal ta lashe kofin kasashen turai sannan kuma ya sake lashe gasar kwararru na shiyyar turai da kungiyar sa ta Real Madrid.
Ronaldo wanda Yaci Kwallaye 59 jimla a shekarar data wuce ya kasance wanda ya lashe gasar wanda yafi kowa iya kwallo a duniya a watan Disambar daya gabata wato Ballon d Or.