Rundunar Ƴan sanda ta shawarci kwankwso ya janye ziyarar da ya shirya kai wa Kano


Rundunar ƴansanda ta jihar Kano tayi kira ga tsohon gwamnan jihar kuma sanata a yanzu, Rabi’u Musa Kwankwaso kan ya dakatar da ziyarar da ya shirya kaiwa zuwa Kano a ranar Talata 30 ga watan Janairu.

Rabi’u Yusif kwamishinan ƴansandan jihar shine yayi wannan gargadi  ya yin wani taron manema labarai ranar Juma’a a Kano. 

Kwankwaso da kuma jam’iyar APC ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun shirya yin wani taron gangamin siyasa daban-daban a ranar 30 ga watan Janairu.

Da yakewa ƴan jaridu jawabi a hedikwatar rundunar dake Bompai a Kano, Yusuf yace bayanan sirri da rundunar ta samu na nuni da cewa wasu ɓatagari za su iya amfani da gangamin na ƴaƴan ɗarikar ta Kwankwasiyya wajen tayar da rikici.

 Ya shawarci Kwankwaso da ya duba yiyuwar ɗage zuwan nasa har sai zaman ɗar-ɗar din da ake ciki a jihar ya ragu.

A satin da ya gabata ne wasu rahotanni ke nuni da cewa Kwankwaso ya ɗage zuwan nasa saboda rashin lafiya da yake fama da ita rahoton da sanatan ya musalta.

You may also like