Rundunar ƴan sanda ta gano gawar ɗaya daga cikin jami’anta biyu da suka ɓace a Benue


Ɗaya daga cikin ƴa sanda biyu da rundunar ƴan sandan jihar Benue ta bayyana bacewarsu an gano shi a mace.

Wasu mutane da ake kyautata zaton fulani makiyaya ne suka kai wa tawagar jami’an ƴan sandan dake sintiri hari inda huɗu daga ciki suka ɓace.

Ƴan sandan na kan hanyarsu ta dawowa daga wani aikin sintiri a wasu ƙauyuka dake karamar hukumar Logo dake jihar.

Amma kuma biyu daga cikin ƴan sandan da suka ɓace sun dawo rundunar ba tare da ko kwarzane ba.

A wata sanarwa ranar Litinin, rundunar ƴan sandan jihar tace  an gano gawar daya daga cikin ƴan sandan wanda aka yanka shi.

Sanarwar ta ƙara da cewa an cire wasu daga cikin sassan jikinsa da suka haɗa da idanu da kuma hanci.

You may also like