Rundunar Soja Ta Ƙaddamar Da Shirin “Gudun Mage” Don Magance Rikicin Manoma Da Fulani


Rundunar Sojan Nijeriya ta kaddamar da wani shiri da ta yiwa lakabi da ” Gudun Mage” na murkushe ayyukan ta’addanci da ke da alaka da rikicin Fulani makiyaya da manoma.

Shugaban Sojan Kasa, Janar Tukur Burutai ya ce za a gudanar da shirin ne a jihohi shida daga ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa 31 ga watan Maris inda ya jaddada cewa sojojin za su tsaurara bincike da kai samame ta hanyar amfani da karfin soja wajen murkushe ‘yan ta’adda.

You may also like