Rundunar Soja Ta Kaddamar Da Atisayen Murkushe Ta’addanci A Kudu Masa GabasRundunar Soja ta kaddamar da wani atisayen wanda ta yi wa lakabi da ‘ Exercise Python Dance’ wato rawar maciji a wani sabon yunkuri na murkushe ayyukan ta’addanci a jihohin yankin Kudu maso Gabas.
Da yake karin haske kan shirin, Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, Kanal Sahir Musa ya nuna cewa manufar shirin shi ne na yaki da masu satar mutane da kuma kungiyoyin fafitikar kafa kasar Biafra wadanda ke barazana ga zaman lafiyar yankin.
Ya ci gaba da cewa shirin zai kuma mayar da hankali wajen ganin an yi bukukuwan karshen shekara lafiya wanda ya haka da na Kirismeti da sabuwar shekara yana mai cewa zai kwashe wata guda ana gudanar da atisayen.

You may also like