Rundunar Soja Ta Kaddamar Da Shirin Fadan Ƙarshe Da Boko Haram


Rundunar Sojan Nijeriya ta kaddamar da shirin karshe na murkushe sauran mayakan Boko Haram inda aka tsara kwashe watannin hudu wajen aiwatar da shirin.

Shugaban Horas da Rundunar Sojan, Manjo Janar David Ahmedu ya ce za a karo Birget shida na sojoji da kayayyakin yaki don samun nasarar shirin inda ya nuna cewa za a fi mayar da hankali ne wajen lalata sansanonin ‘yan Boko Haram din ne tare da ceto mutanen da suka yi garkuwa da su.

You may also like