Rundunar Sojan Nijeriya ta yi raddi ga sabon faifan bidiyon da Shugaban Boko Haram ya fitar a yau inda ta bayyana bidiyon a matsayin wata farfaganda na kungiyar da nufin Jefa fargaba a zukatan mutane.
Da yake tsokaci kan Bidiyon, Kakakin Rundunar, Birgediya Janar Sani Usman ya ce ana ci gaba da bincike kan sahihancin faifan inda ya jaddada cewa a halin yanzu Dajin Sambisa na hannun sojojin Nijeriya kuma suna ci gaba da farautar mayakan kungiyar inda ya shawarci jama’a da su ci gaba da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba.