Rundunar Sojan Najeriya Ta Kubutar Da Sojojinta Biyu Da Akayi Garkuwa DasuHedikwatar rudunar “Operation Delta Safe”, a ran 18 ga watan nan ta samu rahoton garkuwa da aka yi da jami’anta guda biyu a hanyarsu ta zuwa Banki a garin Onelga da ke Jihar Rivers.Rundunar, ta yi nasarar kubutar da jami’ansu guda biyu da aka yi garkuwa da su, tare da kubutar da wasu fararen hula 4 da aka yi garkuwa da su inda daga cikin akwai mace daya.

Baya ga kubutar da jami’anta biyu da wasu fararen hula 4 da rundunar ta yi, ta sake nasarar kama mugayen makamai da wasu kayayyakin tsafe-tsafe.

Haka zalika ta tarwatsa maboyar ‘yan ta’addan duk da dai wasu daga ciki su sun tsere, amma an yi nasarar kama wasu daga cikin wanda aka samu har da matsafa.

Domin cigaba da kama masu aika irin wadannan laifuffuka a fadin kasar nan tare da mikasu ga mahunta don fuskantar hukunci, rundunar sojin najeriya ta bukaci al’uma da su cigaba da samar mata da ingantattun bayanai da zai taimaka wurin gane wadannan ‘yan ta’adda da kuma maboyansu.

You may also like