Rundunar Sojan Nijeriya Ta Bayyana Dalilin Janyewa Daga Garin Dapchi


Rundunar Sojan Nijeriya ta tabbatar da janye dakarunta daga garin Dapchi wanda hakan ya ba mayakan Boko Haram kafar arcewa da daliban Sakandaren garin su 110.

Da yake karin haske kan matakin janye dakarun, Kakakin rundunar Zaman lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu ya ce, an tura sojojin da aka girke garin Dapchi ne zuwa garin Kanama da ke iyakar Nijar da Nijeriya bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kaiwa sojojin Nijeriya da aka girke yankin.

Ya kara da cewa, zaman lafiyar da aka samu a garin Dapchi ne ya karawa rundunar karfin janye sojojin don tallafawa abokan aikinsu da ke fuskantar barazana a Kanama inda ya nuna cewa kafin sojojin su janye sai da suka mika ragamar harkokin tsaron garin ga rundunar ‘yan sandan garin.

You may also like