Rundunar Sojoji sun bayyana sunayen Abubakar Mubi da Malam Nuhu da Malam Hamman cikin manyan kwamandojin Kungiyar da aka hallaka a wannan hari, inda a gefe guda kuma Shugaban Kungiyar Abubakar Shekau ya samu mummunan rauni. Sama da yan Kungiyar 300 ne suka mutu a wannan Harin.
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa hari da mayakan ta na sama suka kai a sansanin BokoHaram ya hallaka wasu jiga-jigan kungiyar, inda suka yi nasarar nakasta Abubakar Shekau da ke cikin masu ikirarin shugabantar kungiyar.
Sanarwa da kakakin rundunar Sojojin Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya fitar a ranar Litinin, na cewa sun kaddamar da hare-hare ne a ranar Juma’ar da ta gabata a kauyen Taye dake yankin Gombale, inda aka jikkata wasu manyan kwamandojin kungiyar.
Sanarwar ta kuma bayyana sunayen Abubakar Mubi, da Malam Nuhu da Malam Hamman a cikin sanarwar, wanda ke nuna cewa mutanen nacikin manyan kwamandojin Kungiyar da aka hallaka a hari. Amma kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin Sojojin, kazalika su ma kungiyar ba su ce komai kan sanarwar sojojin ba.A baya dai Sojojin sun sha ikirarin cewa sun hallaka shugaba Kungiyar Abubakar Shekau sai dai Kungiyar kan musanta ta hanyar wallafa faifen bidiyo da shugaban ke raddi.