Rundunar sojin Najeriya ta ceto mutane 1000 daga hannun yan kungiyar Boko Haram


Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar ceto mutane 1000 dake tsare a hannun yan kungiyar Boko Haram.

Texas Chukwu, mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya,ya bayyana haka cikin wata sanarwa da yafitar ranar Litinin.

Ya ce mutanen da aka ceto sun kunshi mata da yara an kuma ceto su ne daga kauyukan Malamkari, Amchaka, Walasa da kuma Gora dukkaninsu dake karamar hukumar Bama.

Chukwu yace mazan da aka kama an tilasta musu shiga kungiyar ta Boko Haram.

Mai magana da yawun sojan yace mutanen da aka ceto na samun kulawa daga jami’an kiwon lafiya.

Ya kuma nemi sauran jama’a da su kai rahoton duk wani motsi da basu aminta da shi ba.

You may also like