Rundunar Sojin Najeriya Ta Gano Wani Sabon Salo Da Ƙungiyar BokoHaram Ke Amfani Dashi



Rundunar sojojin Nijeriya karkashin ‘operation Lafiya dole’ tace ta gano sabbin salo da ‘yan ta’addan suka dauka na kaucewa harin jiragen sojojin sama da kuma farauto matasa zuwa kungiyar.

Wannan yana kunshe ne a cikin wani sanarwa da kakakin rundunar sojan Kanal Usman Kuka sheka ya fitar, inda yace kungiyar ta jima tana kirkiro dabarun tserewa daga hare hare da jami’an tsaro ke kai musu a ko da yaushe, wanda a cewar sa ya kamata jama’a su san da wadannan dabarun.

Daga cikin dabarun da ‘yan ta’addan suka fitar akwai yanda suke yin rufin gidajen su don kada jiragen sojoji dake farautarsu su gane gida daga sama. Yace suna yin rufin wuraren fakewar su da kwababben suga da laka saboda idan rana ta haska mutum daga nesa ba zai iya gani ba, amma yace rundunar sojoji tuni ta ankara akan wannan basajar ta su.

Kanal Kuka Sheka yace babu shakka shugaban daya bangare na Boko Haram Abubakar Shekau yana cikin matsanancin rashin lafiya. Amma yace Abu Mus’ab Albarnawy wanda yanzu shine yake tashe ta hanyar yaudaran matasa zuwa kungiyar zai shiga hannun su nan ba da jimawa ba. 

Yace bayanan sirri sun tabbatar da cewa yanzu haka ana rudar mutane musamman matasa zuwa shiga kungiyar inda bangaren Abu Mus’ab din ke yaudarar su da cewa suna jihadin gaskiya ne ba irin na daya bangaren ba. Yace wannan ba komai bane illa hanyar rudar matasa saboda duka bangarorin biyu basu da alaka da musulunci.

“Bangaren Abu Mus’ab suna da wakilan su ko ta ina a fadin kasar nan musamman a Arewa maso gabas. Gidan da suke shirya wannan makircin na Potiskum, jihar Yobe, kuma yanzu haka ana kokarin gano gidan nasu.

“Babu shakka Mamman Nur Algadi ya samu rauni ya zama miskini tun shekarar 2014 a garin Mubi, inda jirgin saman sojojin Nijeriya ya kai musu sumame yayin da yake kan babur. Shi Mamman Nur dama ba soja bane a cikin su. Shi daya ne daga cikin majalisar Shura na ‘yan ta’addan. ya samu rauni ne tare da wani Abu Mujahid wanda daga baya Abubakar Shekau ya kashe shi” inji Kanal Kuka-Sheka

A karshe yace saboda wadannan dalilai, ya kamata mutane suyi kaffa-kaffa da rayuwar su lura da yanda ‘yan ta’addan ke kokarin yaudarar matasa zuwa kungiyar su.

You may also like