A kokarin kawo karshen sace-sace musamman na shanu a fadin jihar Zamfara, rundunar soji da aka kafa mai suna “Operation Sharan Daji” a ranar litanin da ta gabata sun yi nasarar kakkabe mazaunan wasu da ake kyautata zaton barayi ne da suka addabi jama’an karamar hukumar Bakura a jihar.
Rundunar sojin, sun kai wannan sumamen ne a dajin Kahiru da ke cikin karamar hukumar Bakura.
Kamar yadda kakakin rundunar sojin najeriya Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya bayyana, ya ce jami’an sojin sun yi musanyan wuta da barayin inda daga karshe suka yi nasaran kashe daya daga cikin barayin.
Daga karshe, ya ce jami’an sojin sun samu shanaye 50, a matsugunar barayin tare da awaki 82 sai kuma tumaki 25.