Rundunar sojin Najeriya za ta kasa sabon sansanin sojin runduna ta 8 a jihar Sokoto da ke arewa maso-yammacin kasar.
Shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriya Laftanal Janar Yusuf buratai ya sanar da cewa, manufar kafa sansanin ita ce, sake samar da tsaro a kan iyaka Najeriya da kasashen waje.
Buratai ya ce, majalisar al’amuran soji ta Najeriya ta amince da a kafa sansanin na runduna ta 8 a Sokoto, kuma za a aike da dakaru daga yankin arewa maso-gabas zuwa sansanin.
Ya ce, da zarar an gama samar da tsaro a yankin arewa maso-gabas to za a tura sojojin zuwa sansanin na Sokoto.