Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da gano gawarwakin sojojinta 16 daga cikin 46 da aka sanar da bacewarsu sama da makonni shida da suka gabata a bakin rafin Yobe da ke arewa maso gabashin kasar.
Babban kwamandan rundunar hare-haren “Lafiya Dole” Manjo Janar Lucky Irabor ne ya sanar da gano gawarwakin sojoji 16 daga cikin sojoji 46 da suka bacen inda ya ce: An tsinci gawarwakin sojojin ne a bakin Rafin Komadogou a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda ya ce daga cikin sojojin da aka gano gawawwakin na su har da ta kwamandan bataliya ta 223 Laftanal Kanal Yusuf.
Janar Irabor ya ci gaba da cewa tuni aka bisne gawarwakin sojojin a makabartar barikin sojojin Maimalari cikin dukkanin girmamawa ta soji.
Wasu rahotanni dai sun ce sojojin sun bace ne a ranar 16 ga watan Oktoba bara (2016) a yankin Gashigar da ke jihar Borno bayan wani mummunan hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai musu, inda aka ce wasu sojojin sun fada cikin kogin ne a kokarinsu na tseratar da rayuwarsu inda ‘yan Boko Haram din suka bude musu wuta da kashe na kashewa da raunata wasunsu a cikin kogin.