Rundunar Sojin Nijeriya Ta Sanar Da Mutuwar Sojoji 5 A Harin Boko Haram


Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa wasu sojojin kasar su 5 sun rasa rayukansu kana wasu 19 kuma sun sami raunuka sakamakon wani harin kwanton bauna da ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram suka kai musu a kudancin jihar Borno.

Rahotanni daga Nijeriyan sun bayyana cewar kakakin rundunar sojin Kanal Sani Usman Kukasheka ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce ‘yan Boko haram din sun kai wa sojojin wannan harin ne a kauyen Ugundiri da ke  karamar hukumar Damboa na jihar Bornon a lokacin da dakarun Operation LAFIYA DOLE suke dawowa daga wajen wani aikin kakkabe mayakan Boko Haram din da suke boye a yankunan Talala and Ajigin da ke kudancin jihar ta Borno.

Sanarwar ta kara da cewa baya ga sojojin da suka mutun, har ila yau kuma wasu ‘yan banga uku da wani mayakin sa-kai guda daya su ma sun rasa rayukkansu yayin wannan harin.

Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun sami nasarar tarwatsa wasu sansanoni da motocin ‘yan ta’addan na Boko Haram kamar yadda kuma suka kwato wasu makamai da suka hada da bindigogi masu kakkabo jirgin sama guda 2 da wasu bindigogi masu sarrafa kansu da wasu gurneti da sauran nau’oi daban-daban na bindigo da albarusai, kamar yadda kuma suka sami nasarar hallaka ‘yan Boko Haram din da aka ce adadinsu ya kai 18.

Sojojin Nijeriyan dai suna ci gaba da samun nasarori a kan ‘yan Boko Haram din lamarin da ya rage musu irin karfin da suke da shi na kai munanan hare-hare.

You may also like