Shugaban rundunar sojojin sama na Nijeriya (NAF) Air Marshal Sadique Abubakar ya bayyana a jiya talata cewa NAF din na kashe naira miliyan 475 kowanne wata wajen sayan man jiragenta da ke yakar kungiyar Boko Haram.
Yayin da yake bude taron dabarun da ta shirya na wannan shekarar, shugaban ya bayyana cewa rundunar na amfani da lita miliyan daya da dubu dari tara a kowanne wata domin ta keta jiragen yakinta a sararin samaniyar arewa maso gabashin kasar, inda Boko Haram su ke.
Ya ce, akan naira 250 kwacce lita, kudaden da rundunar ke kashewa sun kai naira miliyan 475 a duk wata. Ya kara da cewa akwai jiragen da ke shan lita 10,000 a lokaci daya, da wadanda ma ke shan lita 2400 a kowanne awa.
Ya kuma ce, dole sai sun gyara dabarunsu ne za su yi fatan yin ayyukansu na sama yadda ya kamata, domin kawo karshen matsalolin tsaro a Nijeriya. “Dole ne NAF ta yi tsarin da zai tabbatar da samar da man jirage a guraren da ta ke ayyukan” ya ce.