Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Ceto Yan China 7 Daga Masu GarkuwaKakakin Hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gwabket ya shaidawa muryar Amurka cewa, yan kasar Chinan suna aikin hakar ma’adinai a yankin Shiroro, lokacin da masu garkuwa da mutane su ka sace su tun watanni shida da suka wuce, inda aka tafi da su dajin birnin gwari da ake kira Gwaska kusa da Kamfani Doka a cikin jihar kaduna.

Da yake karin haske kan yadda aka bi aka kubutar da yan kasar China, kakakin sojojin saman Najeriyar ya ce dama ana zargin akwai mutane marasa gaskiya a wannan wuri, inda da Asubahi aka shirya wani tsararren farmaki cikin kwarewa da kazar kazar.

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Sojoji na musamman da ga mayakan saman Najeriya sun afkawa wurin da ake garkuwa da mutane, inda yan bindigar su ka bude wa sojojin wuta, nan take suma dakarun suka maida mummunan martini a cewarsu.

Bayan da masu garkuwar su ka tabbatar da sojojin a shirye suka je, hakan ya sa suka zubar da makamansu suka arce, tare da barin mutanen da suke garkuwar da su a baya.

Daga nan an kwashe ‘yan kasar Chinan zuwa sansanin mayakan saman dake Birnion Gwari, kafin daga baya a wuce da su zuwa Babban Asibitin sojojin sama dake Kaduna, domin duba lafiyarsu.

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Air commodore Gwabket ya nanata kudirin Rundunar sojojin saman Najeriya, nayin aiki kafada da kafada da sauran jami’an tsaro wajen ci gaba da kare dukiya da rayukan yan Najeriya da sauran mazauna kasar.

Saurari rahotan cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like